15 Nuwamba 2020 - 14:34
Kakakin Majalisar Shawarar Musulunci Ta Iran Ya Ce; Rikicin Bayan Zabe Ya Nuna Hakikanin Fuskar Amurka

Kakakin majalisar shawarar musulunci ta Iran, Muhammad Baqir Qalibaf, ya fada a yau Asabar cewa; Zaben shugaba kasa na Amurka ya nuna hakikanin yadda kasar take.

ABNA24 : Qalibaf ya kara da cewa; Dan mutuncin da wasu ke ganin Amurka da shi ya rushe, kuma kasar ta hau turbar durkushewa.

Shugaban Majalisar Shawarar musulunci na Iran ya kara da cewa; Yadda Amurka take tallatawa duniya kanta, yana da banbanci matuka da hakikaninta a cikin gida.

Shi dai shugaban kasar Amurka Donald Trump wanda ya sha kaye a zaben da aka yi, ya ki yarda da hakan, labarin da yake a matsayin barazanar fadawar kasar cikin rikici.

342/