ABNA24 : A wata sanarwa da ma’aikatar ta fitar ta ce dakarunta sun sami nasarar cafke Farajollah Chaab wanda aka fi sani da Habib Asyud, shugaban kungiyar ta’addancin nan ta Arab Struggle Movement for the Liberation of Ahwaz (SMLA) biyo bayan wasu samame da ayyuka na sirri da suka gudanar.
Sanarwar ta ce a halin yanzu dai babban wanda ya shirya wannan harin ta’addanci na garin Ahwaz yana hannun jami’an Ma’aikatar kuma ana ci gaba da gudanar da bincike a kansa inda ta ce tuni ya amince da hannun da yake da shi cikin wannan danyen aikin da ma wasu ayyukan ta’addancin da kungiyar ta gudanar yana mai cewa kasar Saudiyya tana daga cikin kasashen da ke daukar nauyin ayyukan ta’addancin da suke gudanarwa.
Har ila yau kuma Chaab ya bayyana wa jami’an tsaron na Iran hannun da kungiyar tasa take da shi cikin wasu ayyukan ta’addanci ciki har da fashi da makami da sauransu. Kamar yadda kuma yayi bayanin shirin da suka yi a baya na kai hare-haren ta’addanci a biranen Tehran da Khuzestan, haka nan kuma a halin yanzu ma suna cikin kai wasu hare-haren ne kafin jami’an tsaron suka sami nasarar kama shi.
A watan Satumban 2018 ne dai kungiyar ta’addancin ta kai hari wajen wani faretin soji da dakarun kare juyin juya halin Musuluncin suke gudanarwa a garin Ahwaz lamarin da yayi sanadiyyar mutuwar mutane 25 cikin su kuwa har da dakarun IRGC din da kuma raunana wasu sama da mutane 70.
Bayanai dai sun nuna cewa Saudiyya da Haramtacciyar kasar Isra’ila su ne manyan masu daukar nauyin wannan kungiya ta ta’addanci da nufin kai hare-hare cikin Iran.
342/