28 Oktoba 2020 - 12:00
Iran Za Ta Ci Gaba Da Shirinta Na Ganin An Kawo Karshen Rikicin Nagorno-Karabakh

Ministan harkokin wajen kasar Iran Dakta Muhammad Jawad Zarif ya bayyana cewar tuni Iran ta fara aiwatar da shirinta na ganin an cimma wata yarjejeniyar sulhu tsakanin kasashen Azarbaijan da Armeniya kan yankin nan na na Nagorno-Karabakh da suke rikici kai.

ABNA24 : Minista Zarif ya bayyana hakan ne a yammacin jiya Talata inda ya ce tuni Iran ta tura wani babban jami’in diplomasiyyarta waje don tattaunawa da bangarorin da abin ya shafa don magance wannan rikicin.

Zarif ya ci gaba da cewa mai yiyuwa a yau din nan Laraba Iran din za ta gabatar da shawarwarinta kan hanyoyin da za a magance rikicin ga jami’an kasashen da suke rikicin da kuma wadanda suke shiga tsakani.

Kafin hakan dai kakakin Ma’aikatar harkokin wajen na Iran Saeed Khatibzadeh ya ce tuni aka nada Abbas Araqchi a matsayin jami’in da zai gudanar da wannan aiki na tattaunawa don cimma sulhun.

342/