ABNA24 : A jiya Litinin ne jigin sama na kungiyar agaji ta “ Red Cross” ya sauka a filin saukar jiragen saman birnin Sana’a, dauke da fursunoni 100 inda kuma aka saki fursunonin makiya 150.
Ana tsammacin kammala musayar fursunonin da su ka kai 1080 a tsakanin bangarorin Yemen da kuma na kawancen yakin da Saudiyya take jagoranta a cikinsu akwai ‘yan Saudiyya da Sudan.
A juma’ar da ta gabata mai dai an yi musayar fursunoni a tsakanin bangarorin biyu da adadinsu ya kai 200.
Saudiyya dai ta shelanta yaki akan kasar Yemen tun a 2015, wanda ya zuwa yanzu ya yi sanadiyyar mutuwar dubban mutane da kuma jikkata wasu dubun dubata. Har ila yau, yakin na Saudiyyar ya yi sanadin lalacewar asibitoci da kuma cibiyoyin shan magani a fadin kasar ta Yemen, da hakan ya kawo cikas a yakin da kasar take yi da cutar covid -19.
342/