15 Oktoba 2020 - 13:21
​Shugaban Kasar Kyrgyzstan Yayi Murabus Sakamakon Ci Gaba Da Tashin Hankalin Da Ke Faruwa A Kasar

Shugaban kasar Kyrgyzstan Sooronbai Jeenbekov yayi murabus daga mukaminsa biyo bayan ci gaba da zanga-zangogi da rikicin da ke faruwa a kasar bayan zaben ‘yan majalisar kasar da aka gudanar wanda ‘yan adawa suka ki amincewa da sakamakonsa.

ABNA24 : A wata sanarwa da ya fitar a yau din nan Alhamis, shugaba Jeenbekov ya ce yayi murabus din ne don hana faruwar fito na fito tsakanin jami’an tsaron kasar da kuma jama’a masu zanga-zanga wadanda suke bukatarsa da yayi murabus.

Shugaban ya ce yana tsoron cewa sojoji da jami’an tsaro za su yi amfani da makamai don kare fadar gwamnatin matukar masu zanga-zangar suka tsaya kyam kan alkawarin da suka yi na fadawa fadar gwamnatin. Don gudun zubar da jini ya sa yayi murabus din.

Tun dai a ranar 4 ga watan Oktoban nan ne kasar Kyrgyzstan ta fada cikin rikici da tashin hankali bayan da aka sanar da sakamakon zaben ‘yan majalisar kasar da aka gudanar inda jami’iyyu masu kusanci da shugaban kasar suka yi nasara, lamarin da ‘yan adawa suka ce ba su yarda ba.

342/