12 Oktoba 2020 - 15:28
​Siriya:Amurka Ta Fara Fidda Danyen Man Fetur Na Sata Daga Arewacin Siriya

Majiyar kamfanin dillancin labarai na gwamnatin kasar Siriya SANA ya bada labarin cewa a jiya Asabar ce gwamnatin kasar Amurka tare da ‘yan ta’adda wadanda take goyon bayansu a yankin Hasaka na arewacin kasar Siriya suka fidda danyen man fetur na sata daga rijiyoyin man a yankin Al-Jazira a karon farko ta kasar Iraki.

ABNA24 : SANA ya kara da cewa tankunan daukar man fetur guda 20 ne makare da danyen man fitur na sata suka shiga kasar Iraki daga lardin Hasaka ta kan iyakar kasashen biyu da ake kira Al-Walid wacce gwamnati bata amince da ita ba.

Kafin haka dai shugaban dakarun kungiyar ‘yan ta’adda ta Kurdawa masu samun goyon bayan Amurka, Mazloom Abdi, ya sanya hannu a kan wata yarjejeniya da wani kamfanin hakar man fetur na kasar Amurka don fara hakar mai daga rijiyoyin aljazeerah na kasar Siriya.

Gwamnatin kasar Amurka dai ta shiga kasar Siriya ne da sunan yaki da yan ta’adda ta Daesh a shekara 2014, amma a halin yanzu tana mamaye da wasu yankunan daga arewacin kasar ta Siriya, tana kuma aiki tare da wasu yan ta’adda a yankin don satar danyen man fetur na kasar zuwa kasashen waje ta kasar Iraki.

342/