ABNA24 : Malama Simo Sadaat –Lari ta kara da cewa abin bakinciki mutane 251 sun rasa rayukansu sanadiyyar cutar a cikin sa’o’ii 24 da suka gabata. Sannan jimillar wadanda suka kamu da cutar tun bayan bullarta a farkon wannan shekarar ya kai 500,075 .
A yayinda jimillar wadanda suka rasa rayukansu sanadiyyar cutar suka kai 28,544. Sai kuma wadanda suka warke daga cutar suka kai 406,389.
A duniya gaba daya dai mutane kimani miliyon 37 ne suka kamu da cutar. Miliyin 28 suka warke, sannan kimani miliyon guda suka rasa rayukansu sanadiyyar cutar.
Kasar Amurka ce a gaba da kimani miliyon 8 na wadanda suka kamu da cutare sannan 219,000 na wadanda suka rasa rayukansu.
342/