ABNA24 : Jaridar Ha’aretz ta HKI ta ba da rahoton cewa a ci gaba da zanga-zangogin nuna kiyayya ga Netanyahun da ake yi, dubun dubatan mutane ne suka fito a garuruwa da yankuna daban-daban na ‘Isra’ila’ don kiran Netanyahun da ake zargi da rashawa da cin hanci da yayi murabus duk kuwa da matakan hana fita da aka dauka don fada da annobar nan ta Coronavirus.
Rahotanni sun ce a birnin Tel Aviv ma daruruwan mutane ne suka taru a dandalin Habima Square suna ta rera taken Allah wadai da firayi ministan.
342/