11 Oktoba 2020 - 13:31
Kungiyar NAM: Wajibi Ne Isra’ila Ta Janye Daga Tuddan Golan Na Siriya

Kungiyar Kasashen ‘Yan Ba Ruwanmu (NAM) ta bayyana cewar wajibi ne haramtacciyar kasar Isra’ila ta girmama kudururrukan Majalisar Dinkin Duniya wajen janyewa daga mamayar da take yi wa Tuddan Golan na kasar Siriya.

ABNA24 : Kungiyar ta bayyana hakan ne cikin wata sanarwar bayan taron ministocin kungiyar da ta fitar inda ta yi kakkausar suka ga ci gaba da mamayar da Isra’ilan take yi wa Tuddan na Golan wanda ta ce hakan wani karen tsaye ne ga dokokin kasa da kasa.

Kungiyar tace wajibi ne a kiyaye hurumin kan iyayokin kasashen duniya kamar yadda dokokin kasa da kasa suka shata tana mai yin Allah wadai da matakan da Israi’ilan take dauka wajen ci gaba da mamaye Tuddan na Golan da ta mamaye su kimanin rabin karnin da ya gabata inda ta ce wajibi ne Isra’ila ta girmama kudurrurrukan kwamitin tsaron MDD da suka bukace ta da ta janye daga yankunan da ta mamayen ta koma zuwa ga kan iyakan da aka shata a shekara ta 1967.

A shekarar 1967 ne dai Isra’ilan ta mamaye Tuddan na Golan bayan yakin kwanaki shida da ta yi da larabawa inda tun daga lokacin ta ci gaba da rike yankin da kuma sauya yanayinsa duk kuwa da kiraye-kirayen da aka ci gaba da yi mata na ta janye daga wajen.

342/