ABNA24 : A cikin wani jawabi da shugaban kasar Venezuela Necolas Maduro ya gabatar a daren jiya, wanda kafofin yada labaran kasar suka watsa kai tsaye, ya bayyana cewa; gwamnatin kasar Colombia na horar da wasu ‘yan daba su kimanin 1000, da nufin yin amfani da su wajen kawo yamutsi a cikin kasar a lokacin gudanar da zabukan ‘yan majalisar dokokin kasar ta Venezula a cikin watan Disamban wannan shekara.
Maduro ya ce a halin yanzu kasar Venezuela kasa ce wadda aka killace ta, ta yadda makiyan al’ummarta suke hankoron ganin bayanta ko ta wane hali,a kan haka dole ne su dauki matakan da suka dace domin kare kasarsu.
Haka nan kuma ya kirayi dukkanin bangarorin tsaro, da suka hada da sojoji da ‘yan sanda kuma jami’an leken asiri, da su zama cikin shirin ko takwana domin tunkarar kowace irin barzana a kan jasar.
Venezuela ta yanke hulda da gwamnatin Colombia tuna cikin watan Fabrairun 2019, bayan da gwamnatin kasar ta shelata amincewa da madugun ‘yan adawa a matsayin shugaban kasar Venezuela.
342/