11 Oktoba 2020 - 13:26
Rauhani Da Putin Sun Tattauna Ta Wayar Tarho Akan Batun Tsagaita Wuta A Yankin Karabakh

Shugaban kasar Iran Dr.Hassan Rauhani da ya tattaunawa ta wayar tarho da takwaransa na kasar Rasha, ya yi maraba da batun tsagaita wutar yaki a Karabakh tare da jaddada cewa ci gaba da tattaunawa akan batun zai kawo karshen rikicin.

ABNA24 : An yi tattaunawar ne dai a tsakanin shugabannin na Iran da Rasha, jim kadan bayan da aka sanar da tsagaita wutar yaki a tsakanin Azerbaijan da Armenia akan yankin Karabbah a yau Asabar.

Bangarorin biyu sun fadada tattaunawa akan halin da ake ciki a yankin na Karabakh da kasashen Azerbaijan da Armenia su ke da sabani akai.

Har ila yau, tattaunawar banagrorin biyu ta tabo yarjejeniyar Nukiliya inda bangarorin biyu su ka jaddada muhimmancin ci gaba da aiki da ita.

A karshe shugaban na kasar Iran ya taya takwaransa na Rasha murnar cikarsa shekaru 68 da haihuwai da ya yi biki akan hakan kwanaki biyu da su ka gabata.

342/