ABNA24 : Kamfanin dillancin labaran IRNA ya nakalto Majid Takht –Ravanchi jakadan Iran a MDD ya na fadar haka a taron kwamitin tsaro na MDD a jiya Litinin da yamma a birnin New York.
Takht-Ravanchi ya kara da cewa kasar Iran a matsayinta na kasa wacce aka yi amfani da irin wannan makamin a kan mutanenta a wannan zamanin ta na yin kira ga dukkan wadanda abin ya shafi da su kowa karshen amfani da wadannan makamai a cikin ko wani hali a duniya.
Jakadan ya kara jadda bukata ga hukuma mai kula, bincike da kuma hana amfani da makaman na guba ta duniya da ta yi adalci a ayyukanta.
Labarin ya kara da cewa dangane da kasar Siriya ya zuwa yanzu an gabatarwa hukumar hana amfani da makaman na guba rahotanni har guda 80 dangane kan cewa ‘yan ta’adda suna son a mafani da irin wannan makaman a kasar ta Siriya amma hukumar bata yi kome ba.
Daga karshe Jakadan ya yi kira ga hukumar ta daina nuna bambanci a binciken da ta ke yi dangane da amfani da irin wadannan makamai a duniya. Ko kuma ta daina aikiwa wasu kasashe banda wasu.
342/