ABNA24 : Shugaban taron na MDD, Bozkir ya bayyana kyakkyawan fata cewa, nan da shekara ko watanni masu zuwa, yana da kwarin gwiwa mambobin kasashe da shugabanninsu za su goya masa baya wajen cimma wannan buri.
Da yake magana game da batutuwa uku wadanda yake son cimmawa a wa'adin jagorancinsa, Bozkir ya ce, na farko, amfani da gargadi a matakin farko, wato samar da matakan dakile yaduwar cututtuka, na biyu, yin hadin gwiwa wajen tinkarar matsaloli, na uku, tabbatar da daidaito wajen samar da allurar rigakafin COVID-19 a nan gaba.
342/