24 Satumba 2020 - 11:19
Nigeria: A Kalla Mutane 23 Ne Su Ka Rasu Sanadiyyar Hatsarin Da Motar Dakon Man Fetur Ya Yi A Garin Lokoja Da Ke Jahar Kogi

Motar dakon man fetur din dai ta yi hatsari ne bayan da matukinta ya kasa sarrafa birkinta da ya lalace, da hakan ya yi sanadin kifewar motar da kuma kama wuta.

ABNA24 : Lamarin ya faru ne dai a kan babbar hanyar Lokoja zuwa birnin taryya Abuja, tare da tashin gobara a cikin motocin da suke kusa daga ciki hadda ta daliban makarantar Polytechnic da suka kone kurmus.

Kafafen watsa labarun jahar ta Kogi sun sanar da mutuwar mutane 20 da su ka kunshi dalibai da kuma masu wucewa ta gefen hanya.

Gwamnan jahar ta Kogi Yahya Bello ya mika sakon ta’aziyyarsa ga iyalan wadanda su ka rasa rayukansu sanadiyyar hatsarin.

Ana yawan samun hatsarin manyan motocin daukar man fetur da suka bin hanyoyin da motocin fasinja ke bi, da hakan yake haddasa asarar rayuka da ta dukiya daga lokaci zuwa lokaci.

342/