23 Satumba 2020 - 10:23
Huthy: Farin Cikin Da Trump Ya Yi Da Kulla Alakar Wasu Larabawa Da HKI, Ya Bayyana Wa Al’ummar Wannan Yankin Gaskiyar Lamurra

Shugaban yunkurin “Ansarullah” na kasar Yemen, Abdulmalik al-Huthy ya bayyana cewa; Masu kulla alaka da HKI, suna amfani da karfi akan al’ummunsu, yayin da su ke kaskantar da kawukansu ga Amurka da HKI. Abdumalik Huthy wanda ya gabatar da jawabi dangane da juyin ranar 21 ga watan Satumba

, ya kara da cewa; A wannan lokacin ana bayyana wadanda su ke riko da hakkokinsu a matsayin masu kiyayya da zaman lafiya.

Har ila yau shugaban yunkurin na “Ansarullah” ya yi ishara da yadda Amurkawa su ka kafawa kasar Yemen kahon zuka da takura ma ta saboda kasantuwarta a bagire mai muhimmanci da kuma rawar da za ta iya takawa a tsakanin al’ummar musulmi.

Bugu da kari, Huthy ya ce; Abinda Amurkan take yi shi ne raba kasar ta Yemen da dukkanin karfin da take da shi, sannan kuma da haddasa rabuwar kawuna a tsakanin al’ummar kasar.

342/