ABNA24 : Har’ila yau majalisar dokokin kasar ta Kuwait ta kara jaddada wannan matsayin a jiya Litini, inda ta ke cewa za ta ci gaba da goyon bayan Falasdinawa har zuwa lokacinda aka kafa kasar Falasdinu a kan iyakar ranar 4 ga watan Yulin shekara 1967 tare da gabacin birnin Kudus a matsayin abban birnin kasar. Da kuma tabbatar da cewa dukkan falasdinawan da aka kora daga gidajensu sun koma gida.
Kafin haka dai shugaban kasar Amurka Donal Trump ya bayyana cewa gwamnatin kasar Kuwait ta na shirin maida huldar jakadanci da HKI kamar yadda Bahrai da kuma UAE suka yi.
Labarin ya kara da cewa maganar shugaban kasar ta Amurka Donal Trump ba ta da inganci ko kadan.
342/