ABNA24 : Kwamandan dakarun kare juyin juya halin musulunci na Iran Manjo-janar Hussain Salami wanda tashar talabijin dina Presstv ta yi hira da shi a daren jiya ne ya bayyana cewa; Dakarun na Iran suna cikin shirin ko-ta-kwana, su karbe ido da duk inda manufofin Amruka su ke a cikin wannan yankin sannan kuma su kone su kurmus.
Salami yana maida martani ne ga barazanar shugaban kasar Amurka Donal Trump na cewa idan Iraniya suka kashe wani Ba’amurka zai rama da hare-hare dubu a kan Iran.
Salami ya kammala da cewa Iran ba zata dauki fansa Shaheed Qasim Sulaimani kan jakadiyar Amurka A Afirka ta kudu kamar yadda Amurkawa suke tsammani ba. Ya ce a lokacinda suke kai hari kan sansanin sojojin Amurka a Ainul Asad, bayan kisan Sulaimani, suna tsammanin Amurka tana jaruntar ramawa, da sannan zata ga maida martani na gaskiya.
A farkon wannan shekarar ne shugaban kasar Amurka Donal Trump ya bada umurnin kissan Shaheed Qasim Sulaimani tare da mataimakin kungiyar Hashadushabi na kasar Iraqi a birnin Bagdaza a ranar 3 ga watan Jenerun shekara ta 2020 da muke ciki.
Manjo Janar Salami ya ambato kalaman wanda ya kafa jamhuriyar musulunci ta Iran, Marigayi Imam Khumaini ( R.A) da yake cewa, Babu wani abu da Amurka za ta iya yi wa Iran.
Kwamandan dakarun kare juyin juya halin musuluncin na Iran ya kuma kara da cewa; Dukkanin dakarun kare juyi, da dakarun sa-kai na Basij, a shirye su ke su sadaukar da kawunansu wajen kare Iran, mutuncinta da tsaronta.
Har ila yau, Salami ya ce; Iran da gaske take akan batun daukar fansa akan dukkanin wadanda suke da hannu kai tsaye wajen kashe Lafatanar Janar Kassim Sulaimani.
342/