ABNA24 : A yau Talata ne za a rattaba hannu akan yarjejeniyar kulla alaka a tsakanin kasashen Hadaddiyar Daular Larabawa, da Bahrain a gefe daya, da kuma Haramtacciyar Kasar Isra’ila a daya gefen, a kasar Amurka.
Wani sashe na kasidar ta jaridar Washingtong Post ya kunshi cewa; A cikin gida Donald Trump yana tsorata al’ummar kasar, yayin da a waje yake nuna cewa yana son sulhunta kasashe.
Kasidar ta ci gaba da cewa; shugaban na kasar Amurka yana son wani abu da zai rike domin yin yakin neman zabe.
Daga cikin mahalarta taron rattaba hannu akan yarjejeniyar a yau a fadar mulki ta Amurka “ White House” da akwai Fira ministan HKI, Benjamin Netanyahu, sai kuma jami’an gwamnatocin kasashen Bahrain da Hadaddiyar Daular Larabawa.
342/