ABNA24 : Masu zanga zangar da suka taru a dandalin Beyazit, rike da kwalayen dake dauke da kalmomin la’anta ga mujjalar ta Charlie Hebdo da kuma shugaba Emanuel Macron na Faransa.
Haka ma masu zanga zangar sun yi barazana ga jaridar dama magabatan na faransa dasu girbi abunda zai biyo baya.
Dama kafin hakan ma’aikatar harkokin wajen kasar ta Turkiyya, ta yi allawadai da kakkausar murya da sabon zaben batancin g amazon Allah, wanda ta danganta da cin mutunci da takalar al’ummar musulmi, bisa fakewa da wani wai yancin fadar albarkacin baki.
342/