12 Satumba 2020 - 13:02
Afganistan : An Fara Tattaunawa Tsakanin Gwamnati Da Taliban

Gwamnatin Afganistan da ‘yan Taliban, sun fara tattaunawar sulhu a wannan Asabar a birnin Doha na kasar Qatar.

ABNA24 : Ana dai kallon tattaunawar mai cike da tsarkakiya, duba da sabanin dake tsakanin bangarorin biyu.

Tsohon ministan Afganistan, kana kuma mai jagorantar tatttaunawar Abdullah Abdullah, ya danganta ranar da mai cike da tarihi, wanda a cewarsa tamakar ranar kawo karshen yaki ne da kuma ukubar da al’ummar kasar ke fama da shi ne.

Haka kuma ya yi fatan samar da tsagaita wuta a matsayin jin kai a kasar.

An dai shafe watanni shida ana dage tattaunawar, sakamakon sabanin da ake da shi tsakanin gwamnatin ta Afganistan da kuma kungiyar ta Taliban, musamman kan batun sakin fursunoni.

342/