ABNA24 : A cewar rahoton kwamitin sulhun MDD, an zabi Nijar domin ta jagoranci taruka guda hudu wadanda zasu bayar da fifiko kan wasu muhimman bangarori, domin aiwatar da tsarin ayyukan kwamitin sulhun bisa gaskiya da inganci.
Jadakan jamhuriyar Nijar a MDD ya ce, hakika, tsarin diflomasiyya shi ne lalibo hanyoyin daidaita al'amurra.
Nijar, ta bakin jakadan na ta a MDD, Malam Abdou Abari, ta ce za ta shirya wani babban taron bidiyo na shugabannin kasashen duniya kan batutuwan da suka shafi zaman lafiya da tsaron kasa da kasa a daidai lokacin da duniya ke fama da annobar korona.
Taron wanda shugaban kasar Mahamadu Isufu zai jagoranta, tare da babban sakataren MDD, Antonio Guteres, da kuma shugaban kwamitin kungiyar tarayyar Afrika (AU) za’a gudanar da shi ne a ranar 24 ga watan Satumban nan yayin zagayowar makon babban taron zauren MDD, wanda a bana zai gudana bisa ga dukkan alamu ta kafar bidiyo.
Jan aikin dake gaban jamhuriyar Nijar, a shugabancin kwamitin tsaron MDD na wannan wata, shi ne takun tsakar dake tsakanin Amurka da Iran, kan yarjejeniyar nukiliyar Iran, wacce Amurka ke son ganin manyan kasashen duniya musamman na turai sun dawo daga rakiyarta.
342/