ABNA24 : Ministan ilimin ya kara da cewa; A shekarar bana bude makarantu tana tattare da matsaloli, amma duk da haka ana kan namijin kokari domin ganin an bayar da ilimi mai nagarta ga dukakkin dalibai, don haka duk wani malamin da yake da tawaya ta fuskar ilimi ta za a dakatar da shi.
Ministan na ilimin kananan makarantu ya ci gaba da cewa; Babu wani nau’i da salon karatu da zai iya maye gurbin wanda ake yi ta hanyar zuwan dalibai makaranta da kansu.
A tsawon watannin da ake fama da cutar Corona a Iran, daliban kan yi karatu ne ta hanyoyin talabijin da kuma internet.
Dangane da matakan zaman lafiya a cikin makarantun, ministan kananan makarantun ya ci gaba da cewa; Nauyi ne a wuyan hukumar makarantu da kuma iyayen yara a kula da kiwon lafiyan dalibai.
342/