ABNA24 : kasrhen yakin basasa na tsawon shekaru bakwai a kasar.
A wani lokaci yau Litini ne ake sa ran rattaba hannu kan yarjejeniyar a birnin Juba na Sudan ta Kudu, koda yake an ce akwai wasu kungiyoyi guda biyu da suka hada da (MLS) da kuma (SPLA-N) da basu sanya hannu ba kan yarjejeniyar a yau, saboda wasu batutuwa da suke da sabani akai.
Sabanin da suke da shi ya hada da batun tsaro, raba arziki da mulki da kuma batun dawo da ‘yan gungun hijira.
Firaministan Sudan Abdalla Hamdok, ya ce yarjejeniyar zaman lafiya da aka shirya rattabawa hannu a yau Litinin, tsakanin gwamnatin kasar da kungiyoyi masu dauke da makamai, mataki ne na farko na samar da dawamammen zaman lafiya a kasar.
342/