ABNA24 : Daga cikin wadanda shugaban kasar zai fara ganawa da su daga ranar Litinin da akwai tsofaffin firai ministoci da su ka hada; Njib Miqati, SDa’adul Hariri, Tamam Salam, sai kuma mataimakin shugaban kasa Ily Farzaly.
Har ila yau, shugaban kasar ta Lebanon Michel Aun zai gana da wakilan jam’iyyun siyasar kasar da su ka hada; al-mustaqbal, da Wafa, lil muqawamah, da kuma Tqaddumi al-ishtraky, da sauransu.
Lebanon ta fada cikin dambaruwar siyasa tun bayan hatsarin da aka samu na fashewar abubuwa a tashar jirgin ruwa ta birnin Beirut, wanda ya kai ga murabus din fira ministan Hasan Diyab.
342/