26 Agusta 2020 - 13:11
Ministan Tsaron Yemen Ya Ce: Makiya Ba Za Su Ci Gaba Da Zama A Cikin Kasar Ba

Ministan tsaron kasar ta Yemen, janar Muhammad Nasir al-Atify ya ce; Matukar muna raye, makiya ba za su ci gaba da zama a cikin kasar Yemen ba.

ABNA24 : Janar al-Atify ya kara da cewa ci gaba da zaman abokan gaba a cikin kasar yana da mummunan sakamako,musamman idan abokan gabar su ka ci gaba da aikata manyan laifuka akan al’ummar Yemen.

Ministan tsaron na kasar Yemen wanda ya gabatar da jawabi a gaban rundunar sojan kasar ya kara da cewa; “ Zancen da muke yi ba kurari ba ne ko barazana,domin mu duk abinda mu ka ambata da fatar baki muna yinsa a aikace.

Ministan tsaron na kasar Yemen ya kuma kara da cewa; A wannan lokacin da ake ciki dakarun tsaron kasar suna aiki da tsarin da zai kai su ga samun nasara, kuma za mu sadaukar da jinanemu da rayukansu domin sake dawo da daukakar al’ummar Yemen.

342/