25 Agusta 2020 - 12:37
Iran Ta Fara Tattaunawa Da Kasar Siriya Don Gina Sabbin Gidaje A Kasar

Mataimakin ministan tsaron kasar Iran da kuma ministan gidaje na kasar Siriya sun tattauna batun gina sabbin gidaje a kasar Siriya a jiya Litinin.

ABNA24 : Kamfanin dillancin labaran IRNA na kasar Iran ya nakalto Ibrahim Mahmood Zade mataimakin ministan tsaron kasar Iran wanda ya ziyarci birnin Damascus a jiya Litinin yana cewa kamfanonin gine-gine a Iran zasu fara aikin gina sabbin gidaje masu kyau da kuma sauki kudi a birnin Damascus babban birnin kasar.

Har’ila yau a bangaren sa Suhail Abdullateef ministan gidaje na kasar Siriya ya bayyana cewa tun shekara ta 2019 kasashen biyu suka rattaba hannu kan sake farfado da rayuwa a kasar Siriya bayan samun nasara a kan ‘yan ta’adda a kasar. Amma yaduwar cutar korona a karshen shekarar da ta gabata ya jinkirta soma aikin.

Ministan ya kara da cewa kamfanonin gine-gine zasu fadada ayyukansu daga babban birnin kasar zuwa sauran lardunan kasar nan ba da dadewa ba.

342/