24 Agusta 2020 - 14:49
Indiya Ta Ce Ta Shirya Fafatawa Da Sojojin China

Jaridar “Bipin Rawat” ta kasar India ta ambato kwamandan sojan kasar India yana cewa; Saboda tattaunawa da kasar China akan sabanin da suke da shi dangane da iyaka a yankin Ladakh, ba ta je ko’ina ba, to New-Delhi ta kammala shirinta na yin fada.

ABNA24 : A makon da ya shude ne dai aka yi ganawa karo ta goma na sha takwas a tsakanin kwamitin da bangarorin biyu su ka kafa da zummar warware sabanin da suke da shi akan iyakar mai tsawon kilo mita dubu hudu.

Watanni biyar kenan da sojojin kasashen biyu suke cikin shirin ko-ta-kwana akan iyaka.

342/