24 Agusta 2020 - 14:43
Hatami : Hulda A Bangaren Soji Tsakanin Iran Da Rasha Na Karfafa Zaman Lafiya

Ministan tsaron na Iran Birgediya Janar Hatami wanda yake ziyarar aiki a kasar Rasha, ya bayyana cewa alakar da ke tsakanin kasashen Iran da Rasha abin koyi ne wanda zai haifar da zaman lafiya das taro a cikin wannan yankin da kuma duniya.

Abna24 : Dangane da sakamakon tattaunawarsa da jami’an kasar Rasha, Birgediya janar Hatami ya bayyana cewa; An cimma matsaya da bangaren Rasha akan ci gaba da tattauanwa akan halayyar turai da Amurka ta son shimfida ikonsu a cikin kasashe da kuma yadda su ka zama masu bakin jini akan hakan.

Birgediya janar Hatami ya kuma yi bayani akan yadda a cikin shekarun bayan nan alakar soja a tsakanin kasashen biyu yake bunkasa,kuma ya ce; “Za mu ci gaba da aiki don fadada alakar”.

A ranar Asabar da ta gabata ne dai ministan tsaron na Iran ya fara ziyarar aiki a kasar ta Rasha a matsayin amsa goron gayyatar da takwaransa ya aike masa Janar Sergey.

342/