ABNA24 : Muhammad Baqir Qalibaf bayyana hakan ne a cikin wasu wasiku guda biyu da aikewa shugaban majalisar dokokin kasar Lebanon nabih Birri, da kuma babban sakataren kungiyar Hizbullah Sayyid Hassan Nasrullah.
Ya ce duniya tag a irin tsayin dakan da al’ummar kasar Lebanon suka yi wajen tunkarar ‘yan mamaya a kan kasarsu, da kuma yadda suka fatattake su, wanda a cewarsa wannan ita ce hanyar rayuwa cikin ‘yanci, ba mika wuya ga makiya a cikin kaskanci ba.
Dangane da hatsarin da ya faru abin Beirut a cikin ‘yan kwanakin da suka gabata kuwa, Qalibaf ya mika sakon ta’aziyyarsa ga dukkanin al’ummar kasar, tare da yin fatan hakan ya zama hanya da zata kara samar da hadin kai domin rusa makircin da ya ce manyan kasashen duniya da ‘yan korensu na yankin suke kullawa Lebanon dare da rana.
342/