15 Agusta 2020 - 12:08
Ivory Coast : Gwamnati Zata Dauki Tsauraran Matakai Kan Masu Bore

Hukumomi a Ivory Coast, sun sanar da cewa zasu dauki matakin ba sani ba sabo, ga masu zanga zangar dake jinin tazarcen shugaban kasar Alhassan Ouatara.

ABNA24 : Gwamnatin kasar ta jan kunnen masu zanga zangar da cewa ba zata rufe ido ba ga masu neman tada hargitsi. Mahukuntan kasar dai na masu zargin wasu ‘yan siyasar kasar na adawa da shirya zangar zangar, duk da kashedin da mahukuntan kasar sukayi na kada a fito zanga zangar. Sanarwar da gwamnatin kasar ta fitar na zuwa ne bayan zanga zanga data barke tun ranar Alhamis, a wasu sassan kasar ta kin jinin sake tsayawa takarar shugaban kasar a karo na uku a zaben shugaban kasar na watan Oktoba mai zuwa.

342/