ABNA24 : A wani bayyani da ya yi wa manema labarai ranar Alhamis, Trump, ya danganta yarjejeniyar da gagarumar nasara tsakanin manyan kawaye biyu, wacce a cewarsa zata kawo karshen zaman dar-dar a gabas ta tsakiya.
Yarjejeniyar a cewar Trump, ta tanadi da dakatar da shirin Isra’ila na mamaye yankunan Falasdinawa.
Shugaban yace nan gaba kadan za’a samu Karin kasashen Musulmin da zasu kulla yarjejeniyar diflomasiya da Israila.
Bayanai sun ce an cimma yarjejeniyar da aka kwashe tsawon anayi, biyo bayan wata tattaunawa da bangarorin uku da suka hada Shugaban na Amurka, da fira ministan Isra’ila, da kuma yarima mai jiran gado na Hadaddiyar Daular Larabawa.
Tuni dai Kungiyar Hamas dake rike da karfin iko a yankin Gaza ta sanar da yin watsi da yarjejeniyar, yayin da Fira ministan Israila Benjamin Netanyahu ya bayyana ranar a matsayin ranar tarihi.
342/