9 Agusta 2020 - 14:31
A Kalla Mutane 8 Ne Su Ka Mutu Sanadiyyar Fashewar Bama-bamai A Sansanin Soja A Kasar Somaliya

A jiya Asabar ne aka sami fashewar wasu bama-bamai masu karfi a cikin barikin soja da ke birnin Mogadishu a kusa da filin kwallo, wanda ya yi sanadiyyar mutuwar mutane 8 da kuma jikkata wasu 14.

ABNA24 : Sojojin da su ke sansanin sun yi harbe-harbe bayan tashin bama-baman. Bugu da kari hayaki ya turnuke samaniyar yankin da aka kai harin, kamar yadda kamfanin dillancin labarun Reuters ya nakalto.

Wani jami’in soja mai suna Abdullahi Mahmud ya fadawa manema labaru cewa; Abinda ya faru hari ne aka kai, ko dai na kunar bakin wake, ko kuma da bama-bamai.

Kakakin kungiyar al-shabab Abdiasis Abu Mus’ab ya sanar da cewa; Harin da mu ka kai na nema shahada ne akan babban sansanin sojan kafirai da ke Magadishu.

Kasar Somaliya dai tana fuskantar hare-hare daga kungiyar ‘yan ta’adda ta al-shabab a tsawon shekaru. Bugu da kari kungiyar tana a matsayin barazana ta tsaro ga kasashen da suke makwabtaka da Somaliya.

342/