4 Agusta 2020 - 12:16
Bolton: Trump Ba Shi Da Mutunci

Tshohon mai bai wa shugaban kasar Amurka shawara akan harkokin tsaron kasa, ya bayyana cewa; Shugaban kasar Donlad Trump mutum ne da ba shi da mutunci.

ABNA: Tsohon mai bai wa shugaban kasar ta Amurka shawara akan harkokin tsaron kasa wanda jaridar “El Payis” ta kasar Spain ta yi hira da shi ya ci gaba da cewa; Abinda kawai Trump ya sanya a gaba a wannan lokacin shi ne yadda za a sake zabarsa, ba abubuwan da su ke da muhimmanci ga Amurka ba.

John Bolton ya kuma siffata shugaban na kasar Amruka da cewa; “ Mutum ne wanda ba shi da mutunci”

Wani sashe na hirar da aka yi da John Bolton din ta kunshi cewa, a lokuta da dama ya sha fadawa shugaban cewa an raba kasar Korea zuwa gida biyu ne tun a 1945, amma ko kadan shugaban bai rike tarihin, kuma ba shi da sha’awar yin nazarin tarihi.

A cikin watan Yuni na wannan shekarar ne dai John Bolton ya rubuta littafi mai taken; A cikin Dakin Da Abubuwa Su Ka Faru’ da a ciki ya yi bayanin raunin shugaba Donald Trump ta fuskar shugabanci.

342/