4 Agusta 2020 - 12:13
Covid-19 : Aljeriya Za Ta Bude Masallatai Ga Jama'a

Shugaban Aljeriya, Abdelmadjid Tebboune, ya sanar ce, kasarsa na duba yuwuwar sake bude masallatai ga jama'a, da suka kasance a garkame yau kusa da watannin biyar sakamakon matakan yaki da annobar korona.

ABNA: Kamfanin dillancin labarai na APS ya ruwaito shugaban na bayyana haka ne yayin wani taron majalisar tsaro, gami da ministoci, domin nazartar yanayin annobar COVID-19 a kasar.

Shugaba Tebboune ya umarci Firaminista Abdelaziz Djerad, ya shirya bude masallatan sannu a hankali.

Ya kara da cewa, da farko, shirin zai bude manyan masallatai 1,000, wanda zai bada damar bayar da tazara tsakanin mutane, sannan dole ne kowa ya sanya takunkumin rufe baki da hanci.

Aljeriya dai na daga cikin kasashen da cutar korona ta fi wa illa a Afrika, inda alkalumman wadanda suka kamu ya kai 31,645 sai kuma 1,231 da cutar ta yi ajalinsu a cewar alkalumman kamfanin dilancin labaren AFP.

Ye zuwa jiya 3 ga wata adadin mace macen da aka samu a nahiyar Afrika sanadiyyar cutar ta COVID-19 ya haura 20,000 yayin da mutanen da aka tabbatar sun harbu da cutar suka haura 950,000, amma akwai wasu sama da dudu 610 da suka warke daga cutar.

342/