3 Agusta 2020 - 13:39
​Mohammad Irfaan Ali Dan Takarar Jam’iyyar Adawa Ya Zama Shugaban Kasar Guyana

Dan takarar jam’iyyar adawa a kasar Guyana Mohammad Irfaan Ali ya zama shugaban kasar Guyana, bayan da aka sanar da sakamakon karshe na zaben da aka gudanar a kasar.

ABNA: Kamfanin dillancin labaran Reuters ya bayar da rahoton cewa, a jiya Lahadia aka sanar da sakamakon karshe na zaben shugaban kasar da aka gudanar a kasar Guyana tun a cikin watan Maris da ya gabata, inda aka sanar da sakamakon farko a cikin watan Yuni, wanda ko a lokacin Irfaan ne a gaba, a jiya kuma aka sanar da sakamakon karshe, wanda ya tabbatar da cewa dan takarar jam’iyyar adawa a kasar Mohammad Irfaan Ali ne ya lashe zaben.

Mohammad Irfaan Ali wanda musulmi ne kuma dan siyasa a kasar ta Guyana da ke kudancin Amurka, ya taba rike mukamin ministan gidaje a kasar, wanda kuam yake da karbuwa a wurin mutanen kasar.

Kasar Guyana wadda adadin mutanenta bai wuce 800,000 ba, tana cikin kasashen duniya masu fama da talauci, inda al’ummar kasar sun dogara ne kawai da noma.

Amma a cikin lokutan baya-bayan nan an gano cewa kasar tana da dinbin arzikin danyen man fetur kwace, wanda kuma nan ba da jimawa ba kasar za ta kasance a cikin kasashen duniya masu arzikin danyen man fetur da ke fitar da shi zuwa kasuwanninsa na duniya.

342/