29 Yuli 2020 - 13:44
Iran : Dakarun IRGC, Sun Kammala Matakin Karshe Na Atisayen Soji

Dakarun kare juyin juya halin musulinci na kasar Iran (IRGC), sun kammala matakin karshe na atisayen sojin da suke a yankin tekun Farisa da kuma mashigar Ormuz.

ABNA24: A sanarwar data fitar rundinar ta IRGC, ta ce an kammala atisayen mai taken ‘‘Rasul A’azam-14’’ da aka kaddara a yau Talata.

Atisayen wanda aka gudanar a yankin Hormozgane, dake yammacin kasar, ya hada dakarun ruwa da na sama.

A yayinsa an nuna wasu sabbin makamai na kariya da makamai masu linzami, da jiragai marasa matuki da kuma kayan soji iri daban daban da kuma nuna bajinta irinta sojojin kasar.

A yayin atisayan sojojin sun gwada tarwatsa wani jirgin ruwan Amurka na bogi da sukayi a kusa da mashigar ruwan Ormuz.

342/