22 Yuli 2020 - 11:20
​Rasha : Ana Shirin Samar Da Alluran Riga Kafin Corona Miliyan 200 A Bana

Kasar Rasha, ta ce tana tunanin samar allurar riga kafin cutar korona miliyan 200 a cikin wannan shekara, idan gwajin da ake kan maganin ya yi nasara.

ABNA24: Zamu iya samar da adadin allura miliyan 200 da mu da abokan huldarmu a cewar Kirill Dmitriev, jagoran asusun Rasha dake bada tallafi kan aikin samar da allurar riga kafin cutar ta Korona, ya shaida a wata hira da shafin Stopcoronavirus.rf.

A Rasha dai an riga an gama matakin farko na gwajin maganin na korona, yayin da kuma ake fatan kammala mataki na biyu wajajen ranar 3 ga watan Agusta mai zuwa.

Za’a kuma kai ga matakin gwajin na uku a kasar ta Rasha, da kuma wasu kasashe da suka hada da Hadaddiyar Daular Larabawa, Turkiyya da kuma a Afrika, sannan baya ga hakan an sarrfa maganin mai yawa inji jami’in, amma kan hakan ana bukatar kasashen su amince da maganin kafin nan da watan Satumba.

Sanarwar da Rasha, ta bayar na zuwa ne kwanaki kadan bayan da kasashen Biritaniya, Amurka da kuma Canada suka zargin jami’an leken asirin Rashar da kutse a ayyukan wasu kungiyoyin kasashensu na samar da riga kafin cutar ta Korona, zargin da Rashar ta musanta tana mai cewa ba shi da tushe balle makama.

342/