ABNA24: Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto shuwagabannin kasashen uku suna wannan barazanar ce bayan taron kasashen kungiyar tarayyar turai EU a birnin Brussels a ranar Asabar.
Labarin ya kara da cewa kasashen a shirye suke su kakabawa duk wata kasar da ta sabawa takunkuman shigar da makamai, ko mayaka cikin kasar ta Libya. Sannan sun yi kira ga bangarorin da suke yakar juna a kasar ta Libya su mutunta yarjejeniyar tsagaiya budeawa juna wata wanda MDD ta samar a kasar.
Kafin haka ma babban sakataren MDD Antonio Guterres ya bayyana cewa shigar da makamai kasar Libya ko tura mayaka daga kasashen waje duk sun sabawa kudurorin majalisar dangane da yaki a kasar ta Libya.
342/