ABNA24: Tashar Russia Today ta bayar da rahoton cewa, mai magana da yawun fadar shugaban kasar Rasha Dmitry Peskov ya fadi a jiya cewa, masana a kasar ta Rasha sun samar da wannan allura ta rigakafin corona, kuma sun yi nasara wajen gudanar ad dukkanin gwaje-gwaje a kanta.
Ya ce a halin yanzu komai yana hannun kwararru na ma’aikatar lafiya ta kasar Rasha, wadanda suke gudanar da nasu aikin a kan wannan allura, kuma umarninsu ne ake jira kafin fara yin aiki da ita a kasar.
Ko a kwanakin baya ma hukumar lafiya ta duniya ta bayyana cewa, tana yin aiki tare da masana na kasar Rasha a kan wannan batu, kuma da zaran allurar rigakafin ta kasar Rasha ta kammala, za a yi aikin hadin gwaiwa tsakanin bangarorin biyu a kan yadda za a amfana da ita.
A daya bangaren kuma kamfanin hada magunguna na kasar Rasha R-Pharm ya sanar da cewa, ya rattaba hannu kan wata yarjejeniya da kamfanin AstraZeneca da ke da mazauni a kasar Burtaniya, wanda ya samar da maganin corona, wanda shi ma a halin yanzu jami’ar Oxford ke aiki kansa domin kara tabbatar da ingancinsa kafin fara aiki da shia duniya.
Kamfanin na Rasha ya kulla yarjejeniya da kamfanin an burtaniya, kan samar da wannan magani a cikin kasar Rasha, da kuma fitar da shi zuwa kasashe 30 zuwa 50 na duniya, domin warkar da wadanda suka kamu da cutar.
342/