(ABNA24.com) Jami’i mai kula da harkokin hulda da jama’a a sansanin sojan na Hamimim, Naval commander Alexander Chervinsky,ya ce sun tarwatsa jiragen biyu marasa matuki da suke dauke da abubuwa fashewa daga nisan kilo mita biyar kafin su isa sansanin.
Jami’in na sojan Rasha ya kuma bayyana cewa; Harin bai haddasa wata asara ta dukiya ko rayuka ba ga sojojin na kasar Rasha.
A cikin watannin bayan nan dai Rashan tana sanar da rusa jiragen sama marasa matuki da ‘yan takafiriyyar ke amfani da su domin kai hare-hare a sansanin soja na Hamimim.
342/