7 Yuli 2020 - 13:01
​Daesh Ta Dauki Alhakin Kisan Fitaccen Masanin Tsaro A Kasar Iraki

Kungiyar ‘yan ta’adda ta Daesh ta dauki alhakin kisan fitaccen masanin harkokin tsaro a kasar Iraki Hisham Alhashimi a daren jiya.

(ABNA24.com)  Kamfanin dillancin labaran Bagdad News ya bayar da rahoton cewa, a cikin sanarwar da ma’aikatar harkokin cikin gidan kasar Iraki ta fitar, ta tabbatar da kisan Hisham Alhashimi.

Rahotanni sun tabbatar da cewa a daren jiya ne wasu mutane da ba a san ko suwane da suka rufe fusakunsu, suka bude wa Hisham wutar bindiga alokacin da yake dawowa gidansa kafin ya fita daga cikin motarsa, ya kuma rasa ransa jim kadan bayan isa da shi zuwa asibiti a cikin birnin Bagadaza.

Hisham dan shekaru 47 da haihuwa, kwararre ne kan harkokin tsaro da kuma kungiyoyin ‘yan ta’adda, kamar yadda kuma ya yi bincike mai zurfi kan lamurra na tsaro, inda ya rubuta littafai a wannan fage.

Kungiyar ‘yan ta’adda ta Daesh ta fitar da sanarwa a yau cewa, ita ce ke da alhakin yi wa Hisham Alhashimi kisan gilla a daren jiya.

Shugaban kasar Iraki barham saleh ya yi Allawadi da kakkausar murya kan wannan hari, tare da bayyana shi a matsayin aiki na ta’addanci, tare da jaddada wajabcin gano wadanda suke hannu a cikin lamarin.

Shi ma a nasa bangare Firayi ministan kasar Iraki Mustafa Kazemi ya yi Allawadai da harin, tare da shan alwashin cewa za a bi sawun wadanda suka aikata hakan, domin kama su da kuma gurfanar da sua gaban kuliya domin su fuskanci hukunci kan abin da suka aikta.

342/