Lamarin dai ya faru ne a ranakun Laraba zuwa Alhamis, a yankin Bankass, dake kusa da iyaka da kasar Burkina faso.
Wani jami’in a yankin wadan bai so a ambaci sunansa ba ya shaidawa kamfanin dilancin labaren AFP, cewa ‘yan bindigan sanya da kakin soji cikin motoci sun farmawa kauyen na ‘yan kabilar Dogon inda sukayi ta bude wuta kan jama’a.
Babu wata kungiya data dauki alhakin kai harin.
Wannan kuma ba shi ne karon farko ba da irin hakan take faruwa a wannan yankin, don kuwa ko a watan Fabarairu ‘yan kauye kimanin talatin ne aka kashe a kauyen Ogossagu, baya ga kazamin harin nan da ya yi sanadin mutuwar fararen hula 160 a ranar 23 ga watan maris na 2019.
342/