29 Yuni 2020 - 07:03
​Dan Takarar “Yan Adawa Ya Lashe Zaben Shugaban Kasar Malawi

Hukumar zaben kasar Malawi ta shelanta dan takarar jam’iyyar adawa ta kasar Lazarus Chakwera a matsayin wanda ya lashe zaben shugaban kasar da aka gudanar a ranar Talatar da ta gabata.

(ABNA24.com)  Hukumar zaben kasar Malawi ta shelanta dan takarar jam’iyyar adawa ta kasar Lazarus Chakwera a matsayin wanda ya lashe zaben shugaban kasar da aka gudanar a ranar Talatar da ta gabata.

Mai shari’a Chifundo Kachale wanda shi ne shugaban hukumar zaben kasar ta Malawi ne ya yi sanarwar a jiya Asaba, tare da cewa; Chakwera ya samu kuri’u 2,604, 043, da hakan ya ba shi kaso 58% na jumillar kuri’un da aka kada.

Shi kuwa shugaba mai ci, Peter Mutharika ya sami kuri’au 1,751, 877 ne, sai kuma Peter Kuwani da ya zo na uku da jumillar kuri’u 33,456.

Tuni magoya bayan jam’iyyar adawa su ka fara bukukuwa na lashe zaben da dan takararsu ya yi.

Zaben da aka yi na ranar Talata ya biyo bayan soke zaben da aka yi ne a watan mayu na 2019 bayan da kotun tsarin mulkin kasar ta tabbatar da an yi magudi domin bai wa shugaban mai ci Peter Mutharika damar yin wa’adi na biyu.


/129