28 Yuni 2020 - 07:35
An Gudanar Da Gangamin Neman Sakin Sheikh Zakzaky A Arewacin Najeriya

‘Yan Shii’a mabiya Sheikh Ibrahim Elzakzagy a birnin Kaduna na tarayyar Najeriya sun gudanar da zanga-zangar neman sakisa a jiya bayan sallar Jumma’a.

(ABNA24.com)  ‘Yan Shii’a mabiya Sheikh Ibrahim Elzakzagy a birnin Kaduna na tarayyar Najeriya sun gudanar da zanga-zangar neman sakisa a jiya bayan sallar Jumma’a.

Kafin haka dai a ranar Laraban da ta gabata ma, ‘yansanda a birnin na Kaduna sun tarwatsa taron zanga-zanga irin wannan a birnin na Kdunu.

Bayan kammala zanga-zangar a jiya Jumma’a dai Shikh Aliyu Tirmizi ya yi jawabi inda ya bukaci gwamnatin Najeriya ta gaggauta sakin sakin malamin da kuma matarsa kamar yadda kotu ta ba da umurni kimani shekaru 5 da suka gabata.

Tirmizi ya kara da cewa mabiyan harkar Islamiya a kasar zasu ci gaba da fitowa don neman a saki malamin duk da cewa gwamnatin tarayyar kasar ta haramta harkar.

Daga karshe Tirmizi ya zargi gwamnatin jihar Kaduna da jan kafa a shari’ar da akewa malam da matarsa don ci gaba da tsaresu na lokaci mai tsawo.


/129