27 Yuni 2020 - 09:17
An Fara Gwajin Allurar Riga Kafin Cutar Korona A Karon Farko A Kasar Afirka Ta Kudu

Jami’ar Wit-waterstrand ta kasar Afrika ta Kudu ta fara gwajin alluran riga kafi ta cutar korona a karon farko a najiyar Afirka.

(ABNA24.com)  Kamfanin dillancin labaran “Reuters” ya bayyana cewa Jami’ar wacce take aiki karkashin Jami’ar Oxford ta fara wannan gwajin a kan mutane ne a ranar Laraba, kuma gwajin yana bukatar masu sa kai akalla 2000 wadanda kuma suke da shekara tsakanin 18 zuwa 65 daga ciki har da wadanda suke fama da cutar Cida ko Aids.

Labarin ya kara da cewa za’a rika kula da wadanda aka yi wa wannan allurar gwajin na tsawon shekara guda don gano yadda maganin yake aiki a jikin mutane daban- daban.

Har’ila yau labarin ya kara da cewa, gwajin shi ne na farko a wajen kasar Britania wanda jami’ar Oxford ta ke gudanarwa. Kafin haka dai jami’ar ta sami mutane ‘yan sa- kai 4000 a kasar ta Britaniya inda ake gwajin allurar riga- kafin.

Farfesa Shabir Madhi, na sashin samar da allurar riga kafi wato (vaccinology) a jami’ar Wits a birnin Joharnasburg na kasar Afirka da kudu ya ce idan sakamakon gwajin yayi kyau, sannan aka yi wa kashi 60% na manya-manyan mutane a duniya za’a shawo kan yaduwar cutar duk da cewa tana nan.


/129