25 Yuni 2020 - 07:21
​Majalisar Turai EU Ta Sake Gargadin Isra’ila Kan Mamayar Yankunan Falastinawa

‘Yan majalisar majalisar dokokin kungiyar tarayyar turai sun sake gargadin Isra’ila dangane da hankoronta na mamaye yankunan Falastinawa da ke yammacin kogin Jordan.

(ABNA24.com)  ‘Yan majalisar majalisar dokokin kungiyar tarayyar turai sun sake gargadin Isra’ila dangane da hankoronta na mamaye yankunan Falastinawa da ke yammacin kogin Jordan.

Kamfanin dillancin labaran MAA ya bayar da rahoton cewa, fiye da ‘yan majlaisar kungiyar tarayyar turai dubu daya ne dagta cikin 1080 suka amince da kudirin da ke gargadin Isra’ila a kan duk wani yunkuri na mamaye yankunan Falastinawa da ke yammacin kogin Jordan.

Bayanin ya ce abin da Isra’ila take neman aiwatarwa yana da matukar hadari, kuma abin da zai biyo bayan hakan ba abu mai kyau a gare ta ba, da kuma makomar siyasarta a yankin gabas ta tsakiya.

Tun kafin wannan lokacin dai kungiyar tarayyar turai ta bayyana matsayinta na kin amincewa da wannan manufa ta Isra’ila, duk kuwa da matsin lambar da Amurka take yi a kan daidaikun kasashen turan na su amince da hakan.


/129