25 Yuni 2020 - 05:43
Qalibaf: Tehran Da Beijin Suna Fuskantar Dagawar Amurka

Shugaban Majalisar shawarar musulunci ta Iran, Muhammad Baqir Qalibaf ya fada a yau Laraba cewa; Tehran da Beijin suna fuskantar halayyar dagawa ta Amurka a cikin bangarori daban-daban, haka nan kuma dabi’arta ta danne hakkokin al’ummu.

(ABNA24.com)  Shugaban Majalisar shawarar musulunci ta Iran, Muhammad Baqir Qalibaf ya fada a yau Laraba cewa; Tehran da Beijin suna fuskantar halayyar dagawa ta Amurka a cikin bangarori daban-daban, haka nan kuma dabi’arta ta danne hakkokin al’ummu.

Shugaban Majalisar shawarar musuluncin ta Iran Muhammad Bakir Qalibaf wanda ya gana da jakadan kasar Sin a nan Tehran, Chang Hua, ya kara da cewa; Alaka a tsakanin kasashen biyu tana da karfi, kuma tana da tsohon tarihi, amma ta kara karfi bayan juyin juya halin musulunci.

Shugaban majalisar shawarar musulucin ta Iran ya kuma jaddada wajabcin ci gaba da bunkasa alakar a tsakanin kasashen biyu.

Muhammad Bakir Qalibaf ya kuma yi tir da yadda Amurka ta ke tsoma baki a cikin harkokin cikin gidan kasashe da su ka hada da kasar Sin. Har ila yau, shugaban majalisar shawarar musuluncin ta Iran ya kuma jinjina wa Sin saboda matsayar da ta dauka akan batun shirin Nukiliya na Iran.

A nashi gefen, jakadan kasar Sin a Iran ya mika wa shugaban Majalisar takardar taya murnar zabarsa da aka yi daga takwaransa na kasar Sin, wacce ta kunshi yadda kasar take a shirye domin bunkasa alaka da Iran.


/129