(ABNA24.com) Yau Talata, ‘yan Malawi ke sake kada kuri’a a zaben shugaban kasar, bayan da kotun tsarin mulkin kasar ta soke waccen zaben da shugaba mai barin gado Peter Mutharika ya lashe.
A zaben na yau ana fafatawa ne a tsakanin shugaba Mutharika da kuma babban abokin hamayyarsa Lazarus Chakwera.
Sakamakon zaben na ranar 21 ga watan Mayu na 2019 da hukumar zaben kasar ta sanar ya nuna cewa shugaba M. Mutharika, ya lashe zaben da kashi (38,57%), yayin da abokin hammayarsa M. Chakwera ya samu (35,41%), na yawan kuri’un da aka kada.
Saidai M. Chakwera, ya yi fatali da sakamakon zaben yana mai danganta shi da mai cike da magudi, kuma a wani lamari na ba zata kotu ta soke zaben, tare da kiran wani sabon zabe.
/129
24 Yuni 2020 - 07:55
Lambar labari: 1049758
Yau Talata, ‘yan Malawi ke sake kada kuri’a a zaben shugaban kasar, bayan da kotun tsarin mulkin kasar ta soke waccen zaben da shugaba mai barin gado Peter Mutharika ya lashe.