(ABNA24.com) - Dakarun Khalifa Haftar sun ce sun kai hari a kain dakarun gwamnatin Tripoli kuma sun kashe wani kasurgumin dan ta’adda, kuma daya daga cikin manyan kwamandojin kungiyar ‘yan ta’adda ta Jabhat Nusra a Syria Ayyub Al-atrash, a wani hari da suka kai kan dakarun gwamnatin Tripoli.
Tashar Russia Today ta bayar da rahoton cewa, a ci gaba da gumurzun da ake yi tsakanin dakarun Haftar da kuma na gwamnatin Tripoli, jiragen yakin dakarun Haftar sun kashe Ayyub Al-atrash, babban dan ta’adda a kasar Syria, wanda yanzu ya koma Libya tare da wasu dubban ‘yan ta’adda, domin taya gwamnatin Tripoli yaki da Haftar.
Tun kafin wannan lokacin dai Haftar ya zargi Turkiya da kwaso dubban ‘yan ta’adda daga Syria zuwa Libya, inda aka girke su a cikin birnin Tripoli, wanda hakan yasa yake kiran gwamnatin Tripoli da gwamnatin ‘yan ta’adda.
/129
22 Yuni 2020 - 09:39
Lambar labari: 1049006
Dakarun Khalifa Haftar sun ce sun kai hari a kain dakarun gwamnatin Tripoli kuma sun kashe wani kasurgumin dan ta’adda, kuma daya daga cikin manyan kwamandojin kungiyar ‘yan ta’adda ta Jabhat Nusra a Syria Ayyub Al-atrash, a wani hari da suka kai kan dakarun gwamnatin Tripoli.