(ABNA24.com) Shafin yada labarai na sabaq ya bayar da rahoton cewa, Abdulramad bin Abdulaziz Sudais shugaban kwamitin kula da haramin makka da madina ya bayyana cewa, sarkin Saudiyya ya amince a gudanar da wasu gyare-gyare a masallacin manzo (SAW) da ke Madina.
Ya ce ayyukan da za a gudanar sun hada da samar da tsari mai aiki da kansa na sauti da kuma wuta gami da na’urorin sanyaya wuri, kamar yadda za a fada wasu bangarorin masallacin, musamman wurin ajiye ababen hawa.
/129
16 Yuni 2020 - 09:28
Lambar labari: 1047212
sarkin Saudiyya ya amince a gudanar da wasu gyare-gyare a masallacin manzo (SAW).